in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen yankin Sahel sun gudanar da taron tsaron kan iyakokinsu.
2013-11-15 10:56:15 cri
A jiya Alhamis 14 ga watan nan ne aka bude taron tattaunawa kan batun tsaron yankunan dake iyakokin kasashen dake Sahel karo na biyu a Rabat, babban birnin kasar Mocorro.

Yayin wannan taro mahalartansa sun cimma matsaya guda, da ta shafi karfafa hadin gwiwar kasa da kasa, don fuskantar kalubaloli, da kuma kiyaye yanayin tsaron yankunan dake kan iyakokin kasashen.

A jawabin sa ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius, ya bayyana cewa, yanayin zaman karko a yankin na Sahel na da muhimmanci ga al'ummar kasashen Turai, kamar yadda yake ga jama'ar kasashen Afirka, hakan ne ma ya sa kasar Faransa, mai da hankali sosai kan harkokin yankin na Sahel, za kuma ta ci gaba da ba da goyon baya ga kasashen yankin, musamman ma kasar Libya, dangane da aikin karfafa tsaron iyakarta, da kawar da kalubalolin dake da alaka da hakan.

Da yake tsokaci kan hakan, ministan harkokin wajen kasar Libya Mohamed Abdul-Aziz ya jaddada cewa, ko wace kasa a duniya ba za ta iya fuskantar kalubalolin tsaro ita kadai ba, kuma kalubalolin tsaron yankin Sahel na barazana ga yankin, tare da haifar da tarnaki ga kasashe makwabta.

Abdul-Aziz ya kuma bayyana cewa, kasar Libya za ta karfafa hadin gwiwa da kasashe makwabtanta a yankin, ta yadda za a dada inganta yanayin tsaron yankunan dake kan iyakoki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China