in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kungiyoyi uku dake karkashin MDD sun dauki niyya domin magance matsaloli a yankin Sahel
2012-04-11 11:20:23 cri
Kungiyoyi uku dake karkashin MDD sun dauki niyya a ranar Talata a birnin Geneva cewa za su yi aiki tare domin magance wasu matsalolin da ka iyar abkuwa anan gaba a yankin Sahel.

Bisa labarin da kungiyoyin agaji suka bayar, an ce kimanin mutane miliyan 15 na fuskantar barazana kuma a cikinsu miliyan 1.5 kananan yara ne 'yan kasa da shekaru biyar.

A cikin watan Disamban shekarar 2011, MDD ta yi kira ga gamayyar kasa da kasa domin samun dalar Amurka miliyan 724 koda yake har zuwa wannan rana kashi 50 cikin 100 na wannan jimilla kadai ne aka samu.

A cewar babban daraktan asusun yara na UNICEF, Anthony Lake, miliyan daya zuwa miliyan 1,5 na kananan yara a wannan yanki na fuskantar matsala mai tsanani ta samun abinci mai gina jiki, matsalar dake iya janyo musu hadarin mutuwa dalilin yunwa ko ciwo.

Yaran da suke fuskantar matsalar kimanin dubu 33 ne a kasar Nijar, dubu 208 a arewacin Najeriya, dubu 178 a kasar Mali kana dubu 127 a kasar Cadi.

Alkaluman da suka shafi Burkina Faso, Mauritanie, arewacin kasar Kamaru da Senegal, sai dai basu shafi kasar Sudan ko Sudan ta Kudu ba inda yake-yake suke kara tsananta matsalar agaji.

A nasa bangare, Antonio Guterres, babban kwamishinan kungiyar dake kula da 'yan gudun hijira ta (HCR) ya nuna cewa matsalar a kasar Mali ta nada damuwa sosai, domin bayan fari da karancin abinci, akwai ricikin siyasa.

Matsalar kasar Mali ta janyo babbar illa, kuma fiye da mutane dubu 200 suka kaura daga wurarensu in ji mista Guterres tare da jaddada cewa hadin gwiwar da kasashe makwabta suka bayar na bude iyakokinsu ya taimaka wajen karbar 'yan gudun hijirar kasar Mali. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China