Shugaban kasar Nijar ya nuna cewa, bisa ga misalin rikicin kasar Mali, yana da muhimmanci mu maida hankali sosai game da babban hadarin ta'adanci da safarar miyagun kwayoyi da ka iya afkawa kasashen shiyyarmu.
Yarjejeniyar sojoji dake tsakanin kasashe wani muhimmin mataki ne dake bisa hanyar habaka dangantaka mai karfi a wannan fanni, in ji shugaba Mahamadou Issoufou.
A nasa bagare, shugaban kasar Mauritaniya ya jaddada cewa, babbar barazanar da ake fuskanta yanzu ita ce daidaituwar zaman al'umma a wannan sabon karni. Idan ka yi la'akari matsalarmu ita ce tsattsauran ra'ayi yana janyo ta'adanci, in ji mista Abdel Aziz.
Kuma ya bayyana wajabcin kasar Nijar da kasar Mauritaniya da ma sauran kasashen dake wannan shiyya da su yi aiki tare wajen yaki da ta'adanci. Cikin hadin gwiwa ne kawai kasashen yankin Sahel za su gudanar da aiki yadda ya kamata kan kalubalolin dake gabansu wanda muhimmin aiki shi ne tsaro, in ji shugaban kasar Mauritaniya da ya isa birnin Yamai a cikin wata ziyarar aiki ta kwanaki biyu. (Maman Ada)