Wani babban jami'in ofishin kula da harkokin jin kan bil adama na MDD (OCHA) a ranar Talatar nan ya yi kira ga al'ummar kasa da kasa da su bada tallafin gaggawa don a samu shawo kan matsalar abinci da abinci mai gina jiki a yankin Sahel na yammacin Afirka, don cimma bukatun jama'a da yawansu ya kai miliyan 11.4 dake fama da matsalar abinci.
Yayin jawabi ga 'yan jarida, jami'in gudanar da harkokin ofishin kula da harkokin jin kan bil adama na MDD na shiyyar Sahel, Robert Piper ya ce, rikici a yankin na kara karuwa kuma suna kara matsowa kusa da kusa, inda sakamakon haka jama'a ke shan wahala matuka, wajen sake farfadowa kafin barkewar wani sabon rikicin.
Ya lura cewa hukukomin jin kai na MDD da sauran wadanda take ayyuka dasu suna barar dalar Amurka biliyan 1.7, don a samu tallafawa miliyoyin jama'a a yankin Sahel, da suka hada da kasashen Burkina Faso, Kamaru, Chadi, Mali, Mauritaniya, Nijar, Gambia da Najeriya.
Sabon jami'in da aka nada ya ci gaba da cewa, a halin yanzu, yankin ya karbi kashi 36 cikin dari kacal na ababai da ake bukata cikin dala biliyan 1.7.
Yace cikin kudade da aka samar, an samar da abinci ga a kalla mutane miliyan daya a wannan shekara, to amma kudade kalilan aka kashe a sauran sassa kamar harkar noma. Piper yace ana cikin mawuyacin hali tare da jadadda cewa, ya dace al'ummar kasa da kasa su ci gaba da samar da kudade masu tsoka saboda samun tallafi a fuska daya, musamman idan akwai dimbin matsaloli ba zai yi wani muhimmin tasiri ba.(Lami Ali)