Da yake karin haske ga manema labaru don gane da wannan ziyara, kakakin babban magatakardan MDDr Farhan Haq, ya ce jagororin Biyu sun yi musayar ra'ayi kan halin da ake ciki don gane da batun tsaro, da ayyukan jin kai a kasar Afirka ta tsakiya, suna masu bayyana bukatar karin kulawar kasashen duniya, don gane da halin da ake ciki a kasar. Haka zalika, Mr. Ban ya jaddada muhimmancin hadin gwiwar dukkanin yankuna, da sassan masu ruwa da tsaki na kasa da kasa, a kokarin da ake yi na tinkarar kalubalen dake ci gaba da fuskantar wannan yanki na Sahel. (Saminu Alhassan)