in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wata babbar tawaga na shirin rangadi a yankin Sahel
2013-11-02 16:34:36 cri
Babban magatakardar MDD Ban Ki-Moon, da shugaban babban bankin duniya Jim Yong Kim sun bayyana shirinsu na ziyartar yankin Sahel cikin mako mai zuwa.

Wannan ziyara ta hadin gwiwa tsakanin manyan jami'an MDD, da na bankin duniya, da wakilan bankin bunkasa nahiyar Afirka, da na kungiyar tarayyar Afirka AU da na tarayyar Turai EU za ta mai da hankali ne ga bankado hanyoyin magance tarin matsalolin dake addabar wannan yanki na Sahel.

Cikin wata sanarwar hadin gwiwa da jami'an Biyu suka fitar a ranar Jumma'a 1 ga watan nan na Nuwamba, sun bayyana yankin na Sahel a matsayin yankin dake fama da kalubalen koma-baya ta fuskar tattalin arziki da tsaro.

Sanarwar ta kara da cewa, babban burin wannan ziyarar hadin gwiwa shi ne lalubo hanyoyin wanzar da zaman lafiya da ci-gaba, batutuwan da a cewar babban sakataren MDDr, ya dace su kasance tare a ko wane hali.

Ana dai sa ran fara wannan rangadi da kasar Mali, daga nan kuma tawagar wakilan ta rankaya Burkina Faso da Chadi.

Wannan dai yanki na Sahel dake kunshe da yawan al'ummar da suka zarta miliyan 80, ya hada kasashen Mauritania, da Eritrea, da Burkina Faso da Chadi, da Niger. Sauran kasashen yankin su ne Nigeria, da Senegal da kuma kasar Sudan.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China