A yayin taron, shugabannin kasashen 5 sun tattauna batun tsaro da samun ci gaba, da yaki da ta'addanci, da sauran batutuwa. Bayan taron kuma, sun sanar da kafa kungiyar kasashe 5 na yankin Sahel don inganta hadin gwiwa a wannan yanki, kuma shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz ya kasance shugaban karba-karba na farko na kungiyar, kuma an kafa sakatariyar a birnin Nouakchott da ke kasar Mauritaniya.
A gun taron manema labaru da aka shirya bayan taron, Aziz ya bayyana cewa, makasudin kafa wannan sabuwar kungiya shi ne, domin yaki da ta'addanci. Ya jaddada cewa, cimma burin samar da tsaro da zaman lafiya shi ne babban aikin wannan kungiya, kuma sai da tsaro kafin a samu sahihin ci gaba. (Bako)