An gudanar da taron tattaunawa kan tasirin rikice-rikicen dake faruwa a yankin Sahel ga kasar Sin
Cibiyar nazarin tsare-tsare a yankin Masar da ofishin jadakancin Sin dake kasar Masar sun gudanar da taron tattaunawa na kasa da kasa a birnin Alkahira, game da tasirin rikice-rikicen dake faruwa a yankin Sahel ga moriyar kasar Sin a nahiyar Afirka, taron da jami'ai da masana daga kasar Sin da kasashen Afirka fiye da 10 suka samu halarta.
Batutuwan da za a tattauna a yayin taron na yini biyu sun hada da halin tattalin arziki da siyasa na kasashen yankin Sahel, da kalubalen da ake fuskanta a fannin kiyaye tsaro, da tasirin da manyan kasashen duniya suke yi a yankin, da rawar da kasar Sin ke takawa a yankin, da kuma yadda za a tabbatar da moriyar kasar Sin a yankuna dake fama da rikice-rikice da dai sauransu. (Zainab)