in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya ba da wani sharhi ta kafar watsa labaran Australia
2014-11-14 16:36:15 cri
Yau Jumma'a 14 ga wata, a yayin ziyararsa a kasar Australia da kuma halartar taron shugabannin kungiyar G20 karo na 9, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya ba da wani sharhi mai taken "a bude sabon shafin dangantakar Sin da Australia" a jaridar Financial Review ta kasar Australia.

Cikin sharhin nasa, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasar Sin na dukufa wajen zurfafa yin kwaskwarima a fannoni daban daban a kasar, kara bude kofa ga kasashen waje da kuma ciyar da aikin gudanar da harkokin kasa bisa doka gaba, domin cimma burin kasar Sin na neman bunkasuwa da farfadowar kasa. Haka kuma ita ma kasar Australia na gaggauta gyare-gyaren tsarin tattalin arziki da kuma kyautatuwar harkokin masana'antu, domin gina kasa mai karfi da wadata. A kan batun harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya kuma, kasashen biyu na ci gaba da karfafa hadin gwiwar dake tsakninsu, ana kuma kara fahimtar juna a tsakanin Sin da Australia. Dalilin haka ne ake sa rai sosai kan hadin gwiwar kasashen biyu, sabo da hadin gwiwar Sin da Australia na da muhimmiyar ma'ana dangane da aiwatar da manyan tsare-tsarensu, kana na da makoma mai haske. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China