Gidan Talabijin na kasa ta Burkina Faso ya gabatar da sanarwar murabus din, shugaba Compaore yana mai kira da a gudanar da babban zaben kasar cikin adalci nan da kwanaki 90.
A yanzu haka ba a san inda tsohon shugaban kasar yake ba bayan da ya yi murabus.
A daya bangaren kuma fadar gwamnatin kasar Faransa ta fidda wata sanarwa, dake bayyana goyon bayan shugaba Francois Hollande game da murabus din shugaba Compaore. Sanarwar ta ce wannan matakin da ya dauka ne hanya mafi dacewa wajen warware matsalar kasar Burkina Faso. (Maryam)