Yayin taron bangarorin biyu sun nuna fatan kara wasu kudurori cikin yarjejeniyar tasu, domin zurfafa hadin gwiwar da ke tsakaninsu, tare da sa hannu kan karin yarjejeniyoyin hadin gwiwa guda 19. A jawabinsa ga mahalarta taron, shugaban kasar Kwadebuwa Alassane Ouattara ya bayyana amincewarsa da sabbin manufofin ci gaba da hadin gwiwa da aka kara cikin yarjejeniyar abokantaka da hadin gwiwa wadda kasashen biyu suka kulla a shekarar 2008. Ya kuma yi imanin cewa dangantaka da hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen biyu za su ci gaba da bunkasa ya zuwa wani sabon matsayi.
Shi ma a nasa tsokaci, shugaban kasar Burkina Faso Blaise Compaore cewa ya yi, an sa hannu kan sabbin yarjejeniyoyin ne don karfafa hadin gwiwa da cinikayyar da ke tsakanin kasashen biyu, da kuma gina hanyoyin mota na zamani, da layin dogo domin jiragen kasa, da kuma raya ayyukan noma da sufuri. (Maryam)