Sanarwar ta nuna cewa, an tsai da kudurin sakamakon samun tashe tashen hankali da zanga-zangar masu adawa da gwamnatin a duk fadin kasar.
Haka kuma, sanarwar ta bayyana cewa, domin magance ci gaban tabarbarewar yanayin siyasa a kasar, shugaba Blaise Compaore da firaminista Luc-Adolphe Tiao sun cimma ra'ayi daya cewa, za a gudanar da babban zaben kasar cikin watanni 12 masu zuwa, kana ana kira ga jama'ar kasa da su dukufa wajen kai zuciya nesa a lokacin sauyin yanayin siyasa, don magance haddasa karin barazana ga yanayin kasar.
A wannan rana, an gudanar da babbar zanga-zanga a kasar Burkina Faso sakamakon yunkurin shugaban kasar yayi na kawo gyaren fuska ga kundin tsarin mulkin kasar don neman yin tazarce. Kuma bisa labarin da jam'iyyar adawa ta kasar ta bayar, an ce, zanga-zanga ta riga ta haddasa rasuwar mutane 30, yayin da wasu fiye da dari suka jikkata.
Dangane da lamarin, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya ba da wata sanarwa ta bakin kakakinsa cewa, yana damuwa sosai don gane da yanayin da kasar Burkina Faso take ciki a halin yanzu, ya kuma yi kira da a dakatar da tashe tashen hankali, da kuma warware dukkanin matsalolin kasar ta hanyar yin shawarwari. (Maryam)