Mahukunta a Nijar sun bayyana amincewarsu da hukuncin da aka yanke, don gane da takaddamar mallakar wani yankin dake kan iyakar kasar da Burkina Faso, matakin da a yanzu ya kawo karshen sa-in-sa, da kasashen biyu ke yi kan wannan yanki tun cikin shekarun 1960 kawo wannan lokaci.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Nijar Morou Amadou ne ya bayyana hakan ga manema labaru ranar Laraba 17 ga watan nan, yana mai cewa, hukuncin da babbar kotun kasa da kasa ta yanke a ranar Talata 16 ga wata, ya fayyace makomar yankin a hukumance da kuma siyasance. Da ma dai tun kafin yanke hukuncin, bangarorin biyu suka bayyana aniyarsu, ta karbar hukuncin da kotun za ta yanke da zuciya daya.
Yayin wata hira wadda wata kafar watsa labaru ta wajen kasar ta watsa, Amadou, wanda shi ne ministan ma'aikatar shari'ar kasar ta Nijar, ya ce, daga yanzu wannan batu ba zai sake zama wani abun damuwa ga bangarorin biyu ba, kuma su ma al'ummomin yankin da abin ya shafa, sun san matsayinsu a hukunce, matakin da ya ce nasara ce ga dukkanin bangarorin biyu.(Saminu)