Shugaban kasar Burkina-Faso Blaise Compaore ya jaddada a ranar Alhamis muhimmancin karfafa yaki da barazanar ta'addanci a yammacin Afrika.
Ya kamata mu sani cewa, akwai barazanar ta'addanci dake kawo babbar matsala a yammacin nahiyar Afrika, kuma tana barazanar ta'addanci ce ta kasa da kasa, dake hannun masu kaifin kishin islama, tare da manyan laifuffukan kasa da kasa, wanda ya kamata mu kafa wata rundunar hadin gwiwa domin magance wannan matsala, in ji mista Compaore a yayin bude taro karo na hudu na dandalin Burkina-Faso da Cote d'Ivoire, da aka bude a birnin Ouagadougou na Burkina-Faso bisa tushen huldar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
A cewarsa, ta'addanci na kasancewa babbar barazana ta fuskar tsaro da zaman lafiya a yammacin Afrika, musammun ma a yankin Sahara inda kungiyoyin kishin islama suke kara aza ikonsu.
Shugaba Compaore da takwaransa na kasar Cote d'Ivoire Alassane Dramane Ouattara sun bayyana gamsuwarsu kan tuntubar juna tsakanin rundunar sojoji da jami'an tsaron kasashen biyu domin hada karfinsu wajen yaki da 'yan fashi da makamai, da kuma yaki da ta'addanci da manyan laifuffuka
Haka kuma shugabannin biyu sun nuna damuwarsu kan hare-haren Boko Haram a Najeriya, da kuma tabarbarewa rikici da rashin zaman lafiya a kasar Afrika ta Tsakiya. (Maman Ada)