in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta baiwa Burkina-Faso kudin sefa biliyan 2.5 domin yaki da fataucin kananan yara
2012-12-25 10:01:06 cri

Kasar Amurka ta ba da taimakon dala miliyan biyar kwatankwacin sefa kimanin biliyan 2.5 ga gwamnatin kasar Burkina-Faso, ta yadda za ta mai da hankalinta sosai wajen yaki da fataucin kananan yara da sa su aikin karfi. A cikin wata sanarwa zuwa ga 'yan jarida da aka fitar a ranar Litinin a birnin Ouagadougou, kasar Amurka ta ba da tallafin dala miliyan biyar ga gwamnatin Burkina-Faso ta hanyar kungiyar "Counterpart International" mai zaman kanta ta kasar Amurka. Tallafin ya shafi warware matsalar aikin karfi da yara ke yi a cikin masana'antun auduga da ma'adinan zinari, tare da mai da hankali a yankunan arewacin Hauts-Bassins, yankin Mouhoun, arewa da tsakiyar arewacin Cascades dake yammacin Ouagadougou. Haka kuma wannan shiri zai taimakawa yara shiga makarantun kwarai da halartar shirye-shiryen horaswa, kuma zai taimakawa iyalai wajen bunkasa hanyoyin karko masu amfani, ta yadda za'a iyar hada su da tsare-tsaren kasa na kare zaman rayuwar jama'a da harkokinsu na yau da kullum. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China