in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta bayyana damuwarta kan halin da ake ciki a Burkina Faso
2014-10-31 10:21:58 cri

Kungiyar tarayyar Afrika (AU) ta bayyana a ranar Alhamis damuwarta sosai kan halin da ake ciki a Burkina Faso. Shugabar kwamitin kungiyar AU, madam Nkosazana Dlamini-Zuma, ta nuna babbar damuwarta kan halin da ake ciki a Burkina Faso, tare da bayyana cewa, tana sanya ido kan yadda abubuwan suke faruwa a wannan kasa dake yammacin Afrika, a cewar sanarwar AU. Madam Dlamini-Zuma ta yi kiran dukkan bangarorin da wannan rikici ya shafa da su maido da zaman lafiya da kuma nuna sanin ya kamata. Haka kuma ta yi kira ga 'yan siyasar Burkina Faso da su kauce wa duk wasu ayyukan tashe-tashen hankali da yin aiki bisa babbar moriyar kasarsu. Shugabar kwamitin ta tura wani rukunin manyan jami'ai da zai kasance cikin tawagar hadin gwiwa zuwa Burkina Faso da ta hada da kungiyar AU, ECOWAS da kuma MDD, domin gudanar da yin shawarwari tare da dukkan bangarori masu ruwa da tsaki na Burkina Faso. A game da haka, shugabar ta yi kira ga hukumomin Burkina Faso da su saukaka zuwan wannan tawagar hadin gwiwa, a cewar wannan sanarwa. Madam Dlamini-Zuma ta kuma tabbatar wa al'ummar Burkina Faso goyon bayan kungiyar AU kan neman hanyoyin siyasa domin warware matsalolin da kasarsu take fuskanta. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China