Wang Min ya bayyana haka ne a yayin da kwamitin babban taron MDD ke gudanar da bincike kan aikin kiyaye zaman lafiyar MDD, ya kuma kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan kiran da babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi game da gudanar da bincike kan ayyukan zaman lafiya da MDD ta aiwatar a dukkannin fannoni. Wang Min ya kara da cewa kasar Sin ta kuma amince da a ci gaba da kyautata muhimman ayyuka, da kuma samu babban sakamako a yayin cikon shekaru 70 da kafuwar MDD a shekarar badi.
Wang Min ya ce, kasar Sin na tsayawa tsayin daka wajen nuna goyon baya da kuma halartar aikin kiyaye zaman lafiya na MDD. A halin yanzu kuma, tawagogin kiyaye zaman lafiya da kasar Sin ta tura wa kasar Liberia na taimaka wa gwamantin kasar wajen yaki da cutar Ebola, haka kuma, kasar Sin za ta tura wasu jirage masu saukar ungulu zuwa kasar Cote d'Ivoire, wannan shi ne karo na farko da sojojin sama na kasar Sin za su halarci rundunar kiyaye zaman lafiyar MDD ta Blue Helmet. Bugu da kari, kasar Sin na son ci gaba da tura 'yan sandan kiyaye zaman lafiya da masana idan akwai bukatar hakan, kana kuma Sin na son ci gaba da nuna goyon baya ga kasashen Afirka wajen karfafa ayyukan kiyaye zaman lafiya da yin hadin gwiwa da gamayyar kasa da kasa ta yadda za a iya ciyar da aikin gaba da kuma ba da gudunmowa wajen kiyaye zaman lafiya da tsaron kasashe daban daban. (Maryam)