A yayin liyafar, ministocin kasashe biyar sun yi musayar ra'ayi da Ban Ki-moon kan batutuwan da suka shafi yaki da ta'addanci, yanayin yankin Gabas ta Tsakiya, yaki da cutar Ebola da sauran batutuwan dake janyo hankulansu matuka, inda suka cimma matsayi daya cewa, a halin yanzu, ana fama da matsaloli a wasu yankunan kasa da kasa, wadanda suka haifar da illa ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. Kuma ya kamata zaunannun mambobi kasashen kwamitin tsaron MDD su dauki mataki na musamman don warware matsalolin, bugu da kari, ya kamata kasa da kasa su yi hadin gwiwa kan wannan batu da kuma goyi bayan aikin da babban magatakardan Ban Ki-moon yake yi kan wadannan batutuwa. (Maryam)