Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Mista Qin Gang ya bayyana a gun taron manema labaru da aka shirya a ran laraba 13 ga wata cewa, a ranar Talata nan 12 ga watan Nuwamba, aka zabi kasar Sin ta zama mambar hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD na wa'adin shekaru uku.
Sin dai na daya daga cikin kasashe 14 bisa kuri'u mafi rinjaye da ta samu, a yayin babban taro karo na 68 na MDD, kuma wa'adin aikinta zai fara ne daga shekara ta 2014 zuwa ta 2016.
Qin ya yi bayanin cewa, wannan zaben ya nuna cewa, kasashen duniya sun amince da kyakkyawan sakamakon da Sin ta samu na raya sha'anin hakkin dan Adam, da kuma mu'ammala da cudanya da kasar Sin take yi cikin yakini tare da sauran kasashen duniya.
Don haka kasar Sin ta nuna godiya ga dukkan kasashen da suka zabi ta na zama mambar hukumar kare hakkin dan Adam ta MDD.(Danladi)