Zaunannen wakilin Sin a MDDr Liu Jieyi ne ya bayyana hakan, yana mai cewa, bisa tsarin da ake kai yanzu, za a yi tarurruka da shawarwari sama da 20 a wannan wata, wadanda suka shafi batutuwa kimanin 20, don gane da harkokin kasashen Afirka da na yankin Gabas ta Tsakiya masu matukar muhimmanci.
Liu ya ce, a matsayin ta na shugaban kwamitin sulhun MDD a wannan karo, Sin za ta yi mu'amala da hadin gwiwa da sauran membobin kwamitin sulhun, da ma bangarori daban daban bisa adalci a bayyane, tare da yin kokari kan daidaita harkokin shiyya-shiyya, dake janyo hankali, tare da sa kaimi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaron duniya.(Fatima)