A cikin jawabinsa, mataimakin ministan harkokin al'adu na kasar Sin Ding Wei ya jaddada muhimmancin kiyaye kayayyakin tarihi a fannin al'adu da aka gada daga kaka da kakanni wajen ba da gudumawa ga ci gaban al'adun ko wace kasa da kuma al'adun kasashen duniya, bugu da kari, ya kuma bayyana bukata da kuma fatansa dangane da hadin gwiwar Sin da Afirka kan kiyaye kayayyakin tarihi a fannin al'adu da musayar ra'ayoyi a tsakaninsu kan wannan fannin.
A nasa bangaren, ministan harkokin al'adu na kasar Zimbabwe Andrew Langa ya yi bayani kan tahiri da kuma halin da kasar ke ciki a aikin kiyaye kayayyakin tarihi na al'adu, ya kuma bayyana ra'ayoyinsa kan yadda za a iya ciyar da hadin gwiwar Sin da Afirka kan wannan aikin gaba, kara wa juna sani kan aikin da kuma yadda za a iya habaka harkokin al'adun Sin da Afirka a nan gaba. (Maryam)