Ministan ma'aikatar al'adu da yawon shakatawa na tarayyar Najeriya Edem Duke, ya ce an zabi jihar Bayelsa dake kudu maso kudancin Najeriya domin daukar bakuncin bikin nune-nunen al'adun nahiyar Afirka da yankin Caribbean, wanda za a gudanar daga ran 5 zuwa 25 ga watan Satumba mai zuwa.
Ministan wanda ya bayyana hakan yayin da yake jawabi gaban mahalarta bikin zaben sarauniyar kyau karo na 26 da jihar ta dauki nauyi ranar Asabar 20 ga watan nan, yace an zabi jihar ta Bayelsa domin gudanar da bikin na bana ne, kasancewarta wata cibiya ta masu yawon bude ido a Najeriya dama fadin nahiyar Afirka baki daya.
Kimanin mutane 7,000 ne dai daga kasashe daban daban, ake sa ran zasu hallara a jihar ta Bayelsa domin halartar bikin na bana.(Saminu)