Gwamnatin kasar Benin na shirin kaddamar da wani kundin dake kunshe da dabarun bunkasa al'adun kasar a kasashen waje, in ji ma'aikatar harkokin wajen kasar Benin a ranar Talata.
Kundin mai kunshe da dabarun bunkasa al'adun kasar Benin zai taimaka wajen kasancewa wani madubi na sabbin dabaru a wannan fanni, in ji ministan harkokin wajen kasar Benin, Nassirou Arifari a cikin wata hirarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
A cewarsa, kundin zai tanadi muhimman matakai shida dake bayyana hakikanan hanyoyin da za'a bi wajen bunkasa al'adun kasar Benin a idon duniya. Musamman ma, in ji ministan, sun hada da kawata ma'aikatu, wuraren tarben baki, dakunan karbar baki da na taruruka na ofisoshin jakadanci da na kananan jakadancin Benin dake kasashen waje da kayayyakin gargajiya dake bayyana al'adun kasar Benin, shirya bukukuwa ko wace shekara kan al'adun kasar Benin a duk inda kasar take da ofisoshin jakadanci da na kanann jakadanci.
Yanzu a duniya, idan wata kasar da ba ta da karfin gabatar asalin al'adunta tare da sauran kasashen duniya, to tana cikin babban hadarin ganin sauran kasashen sun mamaye ta a wannan fanni, in ji mista Arifari tare da bayyana cewa, baya halinsu na musamman na tabbatar da asalin kasa, al'adu kuma sun kasance wata hanyar samun cigaba. (Maman Ada)