in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da bikin makon al'adun Najeriya a birnin Nanjing
2013-10-16 16:37:11 cri

A ranar Larabar nan 16 ga wata ne bikin makon al'adun Najeriya da ake gudanarwa a birnin Nanjing, dake lardin Jiangsu a nan kasar Sin ya shiga rana ta Biyu, inda a yau tawagar jami'ai mahalarta taron daga Najeriya suka yi zama na musamman da manyan jami'an birnin Nanjing da kuma jami'ai daga ma'aikatar raya al'adun kasar Sin.

Yayin zaman na yau, wanda ya samu halartar ministan ma'aikatar raya al'adu da yawon shakatawar tarayyar Najeriya Chief Edem Duke, da mataimakin darakta a sashen lura da cudanyar kasashe a ma'aikatar raya al'adun kasar Sin Zhao Haisheng, an tattauna batutuwa da dama, musamman wadanda suka shafi lalubo hanyoyin bunkasa hadin gwiwar da sassan Biyu ke yi a fagen musayar al'adu.

A jawabinsa yayin zaman tattaunawar na yau mataimakin darakta a sashen lura da cudanyar kasashe, a ma'aikatar raya al'adun kasar Sin Zhao Haisheng, cewa ya yi Nijeriya da kasar Sin sun kafa babban tarihi a fagen bunkasa, tare da musayar al'adu a tsakaninsu. Ya ce kasahen Biyu na daukar matakan da suka dace, wajen bunkasa hanyoyin raya al'adu, tun daga matakin fidda tsare-tsare, ya zuwa gudanar da shirye-shirye, da bukukuwa irin wanda ake yi yanzu haka. Daga nan sai ya yi fatan dorewar wannan dangantaka, wadda ya yi imanin zata taimakawa bangarorin biyu matuka, wajen cin moriyar dake kunshe cikin raya al'adun gargajiya.

Shi kuwa a nasa tsokaci, ministan ma'aikatar raya al'adu da yawon shakatawar tarayyar Najeriya Chief Edem Duke, cewa ya yi irin alakar dake tsakanin kasashen biyu ta zama abar misali ga ragowar kasashen duniya. Duke ya kara da cewa, Najeriya ta tanaji damammaki masu yawa ga wadanda ke son zuba jari a sashen harkokin yawon shakatawa da nishadantarwa. Daga nan sai ministan ya bayyana bukatar kafa yankunan cinikayyar kayayyankin al'adu cikin 'yanci a kasashen biyu.

Wasu daga manyan jami'an hukumomi da cibiyoyin raya al'adun Najeriya da suka halarci zaman na yau, sun gabatar da shawarwari, da suka hada da bukatar karin hadin gwiwar kasashen biyu, wajen gudanar da bikin baje kayayyakin tarihi da na al'adu, da samar da horo ga ma'aikatan cibiyoyin adana kayan tarihi da dai sauran muhimman batutuwa.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China