Shugaba Xi ya yi wannan kiran ne a nan birnin Beijing yayin da yake gabatar da jawabi a bikin cika shekaru 2565 da haihuwar Confucius da kuma taron kungiyar Confucius ta kasa da kasa karo na biyar..
Ya ce, kowa ne bil-adama yana da tsarin musamman na tunani da yadda yake tafiyar da harkokinsu na rayuwa, sannan babu wani tunani ko al'ada da ta fi wata.
Don haka ya ce, wajibi ne kasashe su rika mutunta tunani da kuma al'adunsu, yayin da suke fahimta tare da mutunta al'adun sauran kasashe ba tare da la'akari da girma da karfin kasa ba.
Shugaba Xi ya ce, idan har kasa tana mutunta al'adunta, hakan ba ya nufi ta rufe kofarta ga sauran kasashe ba ne, ko kuma nuna wata manufar ta fi karfin wasu kasashe ba ne. Illa tabbatar da ma'anar, al'ada ta kasancewa tsari na rayuwar kowace kasa. (Ibrahim)