in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da firaministan kasar Indiya
2014-09-18 21:09:09 cri
A yau Alhamis ne shugaban kasar Sin Mr. Xi Jinping ya gana da firaministan kasar Indiya Narendra Modi. Yayin ganawar, shugabannin biyu sun cimma matsaya daya wajen kafa sabuwar dangantakar kut da kut ta sada zumunci tsakanin kasashen biyu, da kuma cimma muraddunsu bisa sabbin zarafi, da samar da zaman lafiya, zaman karko da wadata a nahiyar Asiya har ma da sa kaimi ga shimfida doka da oda mai cike da adalci da daidaici a tsarin zamantakewar al'ummar duniya.

A nasa bangare, Mr. Xi ya jaddada cewa, Sin da Indiya makwabta juna ne masu muhimmanci, kuma a matsayinsu na kasashe masu tasowa mafiya girma kuma kasashen masu saurin ci gaban tattalin arziki, kasashen biyu tamkar wani karfi ne mai muhimmanci ta fuskar sa kaimi wajen samar da madogarai a duniya, ban da haka kuma, a cewarsa, kasashen biyu na kokarin farfado da al'ummarsu tare. Ban da haka kuma, Sin tana daukar kasar Indiya a matsayin abokiyar hadin gwiwa bisa manyan tsare-tsare, yana fatan kara hadin kai da kasar ta Indiya domin kara zurfafa dangantakar dake tsakaninsu, tare kuma da habaka hadin kai a tsakaninsu da shiyya-shiyya da kuma a duniya baki daya. Kazalika, game da wannan batu, Mr Xi ya ba da shawarwari hudu ta fuskar jagoranci da shugabannin biyu za su bayar.

A nasa jawabin, Mr Modi ya ce, hadin gwiwa da samun bunkasuwa tare tsakanin kasashen biyu, ba ma kawai jama'ar kasashen biyu za su ci gajiyarsa ba, har ma zai ba da gudunmawa sosai wajen samar da zaman lafiya da wadata ga nahiyar Asiya da duniya, har ma ga ci gaban Bil Adam. Ban da haka kuma, Mr Modi ya jaddada matsayin da Indiya ke dauka na amincewa da yankin Tibet a matsayin wani bangaren kasar Sin, kuma ba za ta yarda a aikata wani abin a Indiya da zai kai ga fitar da shi daga babban yankin kasar Sin ba ko kadan. Dadin dadawa, Indiya na fatan hadin gwiwa da Sin wajen daidaita duk wani cece-kuce kan harkar iyakokinsu, da kuma sa kaimi ga shawarwari kan wannan batu, ta yadda za a samar da wani shiri na warware maganar cikin hanzari. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China