Shugaban Sin Xi Jinping, da takwaransa na Myanmar U Thein Sein, da mataimakin shugaban kasar Indiya sun halarci wannan biki. A cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana ra'ayin Sin kan nacewa ga bin manufar zama tare cikin lumana da sa kaimi ga kafa sabuwar dangantaka tsakanin kasashen duniya a sabon zamani, ciki har da tsayawa tsayin daka kan tabbatar da adalci a fannin ikon mallakar kasa, tabbatar da tsaro tare da juna, samun bunkasuwa tare, yin hadin gwiwa domin samun moriyar juna da sauran manyan manufofi masu muhimmanci.
Bayan haka, shugaba Xi ya furta cewa, Sin za ta tsaya tsayin daka kan neman samun bunkasuwa cikin lumana, kuma babu wata kasar da za ta canza ra'ayinta ba ko kadan.(Fatima)