in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya kai ziyara jihar Gujrat ta kasar Indiya
2014-09-18 10:01:18 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai ziyara jihar Gujrat dake kasar Indiya a ranar 17 ga watan nan, bisa rakiyar mai masaukin sa firaministan kasar ta Indiya Narendra Modi.

Yayin wannan ziyara shugabannin biyu sun gana da juna tare da ziyartar dakin marigayi Mahatma Gandhi, da wurin yawon shakatawa na gabar kogi da ake ginawa. Lokacin tattaunawar ta su shuwagabannin sun tabo batu game da raya dangantakar dake tsakanin kasashen na su, da sauran manyan batutuwa.

Shugaba Modi ya karbi shugaba Xi Jinping hannu biyu-biyu, ya na mai bayyana cewa zangon farko da shugaba Xi Jinping ya kai ziyara a kasar Indiya shi ne garinsa na haihuwa wato jihar Gujrat, jihar da jama'ar ta  suke yi matukar farin ciki da ziyarar ta shugaba Xi.

Mr. Modi ya ce kalaman sa na "kasashe biyu masu tunani daya" da ya taba bayyanawa tana yaduwa a fadin kasar Indiya. Kuma kasashen Indiya da Sin suna da burin samun bunkasuwa iri daya, babu shakka kuma za su kara yin hadin gwiwa da juna.

A nasa bangare, Xi Jinping ya bayyana cewa, kasashen biyu kasashe ne dake dab da juna, kuma suna cikin kasahen dake da al'adun gargajiya a duniya, kuma manyan kasashe ne masu tasowa, dake kokarin samun farfadowa da bunkasa. Don haka ne a cewarsa ya dace su girmama juna, su yi koyi da juna, su sada zumunta tare da kokarin samun bunkasuwa tare.

A cewar shugaba Xi na kasar Sin ziyararsa a wannan karo ziyara ce ta sada zumunta da bunkasa hadin gwiwa. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China