Wannan ita ce ziyarar shugaba Xi ta farko zuwa kasar ta Indiya tun lokacin da ya kama aiki a watan Maris na shekarar 2013, kana ziyara ta farko da wani shugaban kasar ta Sin ya kai kasar ta Indiya a cikin shekaru 8.
Yayin ziyarar ana saran shugaba Xi ya halarci wasu taruka tare da Modi a garin na Amedabad a yau laraba kafin ya koma New Delhi,babban birnin kasar ta Indiya.
Bugu da kari a lokacin da ya ke kasar Indiya, ana sa ran shugaba Xi ya gana da takwaransa na Indiya Pranab Mukherjee da sauran shugabannin siyasar kasar, zai kuma gabatar da jawabi a New Delhi game da hadin gwiwar Sin da Indiya da kuma manufar Sin game da kudancin Asiya.
Indiya ita ce zangon karshe na ziyarar da shugaba Xi ya ke a kasashe 4 na tsakiya da kudancin Asiya, inda tuni ya ziyarci kasashen Sri Lanka, Maldives, da kuma Tajikistan, inda ya halarci taron kolin kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai(SCO). (Ibrahim)