Sharhin wanda jaridun "The Hindu" da kuma "Dainik Jagran" suka buga ya kunshi tsokacin shugaba Xi, ciki hadda tsokacin da ya yi game da babban ci gaban da ake samu game da dangantakar dake tsakanin Sin da Indiya a sabon karni.
Ya ce kasar Sin ta kasance abokiya ga Indiya, wadda ke cikin kasashen duniya mafiya girma a fannin cinikayya. Kana kasashen biyu suna hadin gwiwa wajen tinkarar sauye-sauyen yanayi, da tsaron abinci, da tsaron makamashi da dai sauran kalubalen duniya. Kaza lika shugaba Xi ya kara da bayyana irin ci gaba da ake samu a fannin shawarwari da bangarorin biyu ke yi game da batutuwan kan iyakokinsu.
Bugu da kari shugaba Xi Jinping ya bayyana fatansa game da dorewar musayar ra'ayoyi tsakaninsa da shugabannin kasar Indiya a yayin ziyararsa ta wannan lokaci, tare da kara raya dangantakar abokantakar dake tsakanin kasashen biyu ta zaman lafiya da wadata. (Zainab)