A yayin ganawar, Li Keqiang ya ce, moriyar kasashen Sin da Indiya ta bai daya ta fi sabanin da ke tsakaninsu. Kasar Sin tana son yin kokari tare da Indiya wajen warware batun iyakar kasashensu ta hanyar yin shawarwari kuma cikin lumana, a kokarin samar da kyakkyawan yanayi wajen yin hadin gwiwa a tsakaninsu.
Har wa yau Li Keqiang ya ce, sabuwar gwamnatin kasar Sin tana mai da hankali kan raya dangantaka a tsakaninta da Indiya, tana son inganta amincewa da juna ta fuskar siyasa a tsakaninta da Indiya, zurfafa hadin gwiwar da ke tsakaninsu, da kara yin tuntubar juna a kan al'amuran kasa da kasa, a kokarin kiyaye da raya dangantakar yin hadin gwiwa da abokantaka a tsakanin kasashen 2 bisa manyan tsare-tsare.
A nasa bangaren kuma, Salman Khurshid ya ce, kasar Indiya tana son hada kai da kasar Sin wajen nuna wa kasashen duniya tabbacin- cewa, kasashen 2 na amincewa da juna da mara wa juna baya, sa'an nan za su tinkari sabanin da ke tsakaninsu yadda ya kamata, a kokarin warware batun iyakar kasashensu yadda ya kamata.(Tasallah)