A yayin ziyarar, shugaban kasar Sin Xi Jinping da firaministan kasar Li Keqiang za su gana da shi, kuma Li Keqiang zai yi shawarwari tare da shi. Ban da wannan kuma, Singh zai yi jawabi a makarantar horar da jami'an kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. (Zainab)