Shugaba Robert Mugabe na Zimbabuwei, ya bayyana goyon bayan sa ga dokar yaki da soyayya, ko auren jinsi guda, wadda kasar Uganda ta sanyawa hannu a 'yan kwanakin baya, inda a fakaice ya nuna cewa, kasarsa za ta daura yaki da kungiyoyin dake kare 'yan luwadi da madugo a kasar.
A ranar 3 ga watan nan ne dai jaridar Herald ta gwamnatin kasar Zimbabuwei, ta rawaito shugaba Mugabe yayin murnar bikin auren 'yar sa na cewa, dokar yaki da soyayyar jinsi guda, da shugaban kasar Uganda Yori Museveni ya sanyawa hannu, wani yaki ne da yake yi bisa adalci.
Ya ce amincewa da soyayyar jinsi guda bisa doka, tamkar wulakanta dangantakar aure tsakanin maza da mata da ubangiji ke karewa ne. Mugabe ya ci gaba da cewa, Zimbabuwei ba za ta yarda yaranta, su girma a cikin wani yanani na amincewa soyayyar jinsi guda bisa doka ba.
A watan Fabrairun wannan shekara ne dai shugaba Museveni, ya sa hannu kan dokar ta yaki da soyayyar jinsi guda a hukunce, inda aka tabbatar da cewa, irin wannan soyayya ta saba wa dokar kasar, wanda za ta janyowa wanda aka kama da sabawa dokar hukuncin daurin rai da rai a kurkuku.
Game da hakan, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon, ya bayar da wata sanarwa, dake nuna cewa zai sanya ido kwarai kan wannan batu. Haka nan kasar Amurka ta goyi bayan daukar matakin dakatar da baiwa kasar ta Uganda taimakon kudade sakamakon wannan doka. (Danladi)