Wata sanarwar da fadar shugaban kasar Uganda ta bayar ta bayyana cewa, shugaba Museveni ya gana da jakadan kasar Amurka dake kasar Uganda Scott DeLisi a fadar shugaban kasar dake da nisan kilomita 40 a kudu da birnin Kampala, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan taron kolin da ya gudana tsakanin Amurka da kasashen Afirka a kwanakin baya.
Museveni ya bayyana cewa, ita ma kasar Amurka tana da nata matsalar, don haka tilas ne ta warware matsalarta da farko kafin ta yi la'akari da matsalolin sauran kasashe.
Ya ce, taron kolin yana da ma'ana, amma matsalar ita ce wasu kasashen sun yi tsammani cewa Amurka za ta iya warware dukkan matsalolin da Afirka ke fama da su.
Ban da wannan kuma, Museveni ya kara da cewa, idan Afirka ta samu taimako a fannonin samar da kayayyakin more rayuwa kamar hanyoyin jiragen kasa, hanyoyin mota, da samar da wutar lantarki da dai sauransu, to za ta samu karfi wajen canja tsarin tattalin arzikinta. Kana yana fatan gwamnatin kasar Amurka za ta taimakawa kasarsa wajen gina hanyoyin jiragen kasa da suka hade gabashin Afirka da kasar Congo Kinshasa, da kuma wadanda suka hade kasar Habasha da Masar, hakan zai saukaka wa kasashen Afirka wajen gudanar da harkokin cinikayya a tsakaninsu.(Zainab)