A lokacin ganawar, Mr Li Keqiang ya nuna cewa, Sin da kasashen Afrika kasancewar kasashe masu tasowa a duniya, suna da buri iri daya na neman samun 'yancin al'ummar su da kuma bunkasuwar kasar su. Hakan ya sa Sin za ta ci gaba da goyon bayan wanzar da zaman lafiya da samun bunkasuwa a nahiyar Afrika, da kare dankon zumunci dake tsakanin bangarorin biyu, sannan ta ingiza hadin kai tsakanin su.
A don haka a cewar sa yana fatan kai ziyara a nahiyar a cikin wannan shekara da muke ciki, domin sa kaimi ga samun habaka dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu bisa sabon zarafi mai kyau.
Ban da haka kuma, Mr Li ya nuna cewa, a matsayin mai kiyaye zaman lafiyar duniya kuma mai sa kaimi ga samun bunkasuwa tare, MDD ta sauke nauyin dake wuyanta na kiyaye ka'ida mai tushe dangane da dangantakar kasa da kasa saboda haka kasar Sin za ta ci gaba da marawa wa majalisar baya wajen ganin ta kara ba da gudunmawar ta, ta yadda za ta mai da muhimmanci kan samun cigaban shirye-shiryen ta na bayan shekarar 2015. Wadanda za su sa kasashen Afrika su ci gajiya.
A nasa bangare, Mr Sam Kutesa ya bayyana cewa, Sin ta tallafawa kasashen Afrika domin ganin sun samun 'yancin al'umma da kuma bunkasuwar kasashen su, sannan ta nace ga kiyaye moriyar kasashen Afrika cikin harkokin kasa da kasa, abin da ya nuna cewa, kasar Sin sahihiyar kawa ce ta kasashen Afrika. (Amina)