in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
WHO ta kira taron gaggawa don fuskantar matsalar yaduwar cutar Ebola
2014-08-07 11:09:18 cri
Bisa sabon labarin da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayar jiya Laraba 6 ga wata, an ce, ya zuwa ranar 4 ga watan Agusta, yawan mutanen da suka kamu da cutar Ebola mai saurin yaduwa ya kai 1711, kana 932 daga cikinsu sun rasu, bisa kididdigar da kasashen Guinea, Liberia, Saliyo da Nijeriya suka bayar. Wannan ya sa hukumar ta kira taron gaggawa a jiya don tattauna matakan da za a dauka wajen hana yaduwar cutar Ebola.

Hukumar ta kuma bayyana cewa, ya zuwa yanzu, an fi samu rasuwar rayuka a kasar Guinea, yayin da kasar Saliyo ta kasance kasar da aka fi samun mutanen da suka kamu da cutar.

A wannan rana, manyan jami'an hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, wasu jami'an kasashen dake fama da cutar da kuma wasu masanan kiwon lafiya na kasa da kasa sun halarci taron na gaggawa da WHO ta kira a asirce.

Za a kashe kwanaki biyu ana gudanar da taron, sai dai ba za a gabatar da sakamakon taron ba har sai a ranar 8 ga wata.

Kana bisa labarin da hukumar WHO ta samar, an ce, idan har taron ya tabbatar cewa, cutar Ebola da ake ciki a halin yanzu ta kasance lamarin kiwon lafiyar jama'a ta gaggawa dake janyo hankulan kasa da kasa, to za a gabatar wa babbar sakatariyar WHO Margaret Chan Fung Fu-chun matakan gaggawa da za a dauka kan wannan cuta. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China