Gwamnatin Nigeria ta fara binciken lafiyar fasinjojin jiragen sama da suka fito daga kasashen da ke fama da cutar Ebola domin murkushe yaduwar cutar a Nigeria.
Kakakin hukumar jiragen sama ta Nigeria Yakubu Dati, wanda ya bayyana hakan a yayin wata zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a birnin Ikko, inda ya ce, ana sa ido tare da binciken fasinjojin jiragen sama a filayen saukar jiragen sama na kasa da kasa dake Nijeria.
Yakubu Dati ya kara da cewa, dukanin fasinjojin da suka ratsa ta kasashen dake fama da cutar Ebola ana bincikar zafin jikinsu da wata na'ura ta hannu.
Kakakin hukumar jiragen samar ta Nigeriya ya ce, a nan gaba ana sa ran cewa, jiragen sama za su haramtawa fasinjoji marasa lafiya shiga jiragensu, sai dai idan suna dauke da sahihin rahoto na lafiyarsu. (Suwaiba)