A hannu guda kuma wani jami'in hukumar kiwon lafiyar kasar ya bayyana cewa, ya zuwa ranar 2 ga watan Agustan nan, adadin mutanen da ake zaton sun kamu da cutar ya kai 2497.
Kawo yanzu, cutar Ebola na daya daga cikin cututtukan da suka fi saurin kisa a dukkanin fadin duniya, kana ba a kai ga samar da magani ko rigakafin kamuwa da ita ba.
Wani rahoton da kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa ta fitar a ranar 4 ga watan nan ma ya nuna cewa, ya zuwa ranar 1 ga watan Agustan nan, cutar ta Ebola ta riga ta hallaka mutane 887 a kasashen dake yammacin Afirka, kana yawan mutanen da aka tabbatar sun kamu, da wadanda ake zaton sun kamu da ita sun kai 1603. (Maryam)