Ministan lafiya na kasar Nigeria Onyebuchi Chukwu ya ce, likitan da ya duba lafiyar wani dan kasar Liberia mai dauke da cutar Ebola a birnin Legas, shi ma a halin da ake ciki cutar ta kama shi.
Ministan ya ce, a halin da ake ciki ana binciken lafiyar wani likita na daban, wanda shi ma ya duba lafiyar mai dauke da cutar domin a gano ko shi ma cutar ta kama shi.
Likitocin guda biyu sun duba lafiyar Patrick Sawyer, wani dan kasar Liberia, wanda a karshe ya mutu a Nigeria, kusan makonni biyu da suka wuce, a sakamakon kamuwa da cutar Ebola.
Ministan lafiyar na Nigeriar ya ce, an baiwa jiragen kasashen waje umurni, da kar su sake shigo Nigeria da gawarwakin mutanen da suka mutu a sakamakon cutar Ebola daga wasu kasashe.
Hukumomin na Nigeria dai sun ce, ba za su rufe kan iyakarsu ba a sakamakon cutar Ebola, wacce ba ta da magani, sai dai idan yin hakan ya zama dole. (Suwaiba)