Kasashe goma sha biyar na kungiyar ci-gaban tattalin arzikin gabashin Afrika SADC suna cikin shirin ko-ta-kwana domin fuskantar barazanar cutar Ebola tare da gudanar da wani taron gaggawa a yayin da wannan cuta take ci gaba da zama wata babbar annoba a yammacin Afrika.
Sakataren kungiyar SADC ya bayyana a ranar Talata a birnin Gaborone cewa, ministocin kiwon lafiya na shiyyar sun kira wani taron gaggawa a birnin Johannesburg na kasar Afrika ta Kudu, a kokarin fuskantar barazanar annobar Ebola.
An samu wasu mutanen dake dauke da kwayoyin cutar Ebola a kasar Guinee dake yammacin Afrika a cikin watan Maris na wannan shekara. Kwayoyin cutar na yaduwa cikin sauri duk da kokarin da ake a wurin, haka kuma cutar ta shafi wasu kasashe makwabta
Ganin cewa ita ce annoba mafi tsanani a tarihi tare da barazanar yaduwa a shiyyar gabashin Afrika, dalilin haka ne, ministocin kiwon lafiya na yankin suke shirin halartar wani taron musamman na yini guda a ranar Laraba kan cutar Ebola.
Tun bayan bullowar annobar Ebola, sakatare janar na kungiyar SADC zai kira wani taron gaggawa na yini guda na ministocin kiwon lafiya na kasashe mambobi goma sha biyar na kungiyar SADC da abokan huldarta a Johannesburg na Afrika ta Kudu a ranar 6 ga watan Augustan shekarar 2014, in ji sakataren kungiyar SADC a cikin wata sanarwa.
Babban makasudin wannan taro shi ne na tattara ministocin kiwon lafiya da masu ruwa da tsaki domin kafa wani shirin da ya dace wajen rigakafin shiga da yaduwar cutar Ebola a shiyyar SADC, in ji wannan sanarwa. (Maman Ada)