in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hanyar jiragen sama tsakanin Liberiya da Ghana na ci-gaba da aiki
2014-08-06 14:42:12 cri

Kasar Liberiya dake fama da annobar cutar Ebola ta karyata rahotannin dake bayyana cewa, akwai yiwuwar gwamnatin kasar Ghana ta hana jiragen saman kasarta zuwa Liberiya da kuma na Liberiya zuwa kasar Ghana.

Sabbin rahotannin da wasu kafofi suka watsa sun ce, kamfanonin jiragen sama na Kenya Airways, Gambia Bird da ma wasu sauran kamfanoni na ci gaba da jigilarsu zuwa Monrovia da Ghana, in ji wata sanarwar ma'aikatar harkokin wajen Liberiya.

Babu wani matsin lamba ko tsare fasinjojin Liberiya a filin jirgin kasar Ghana, in ji wannan sanarwa.

Haka kuma sanarwar ta kimanta wadannan rahotannin da jita-jita da rashin gaskiya dake nuna cewa, gwamnatin Ghana ta hana jiragen dake fitowa daga kasashen Liberiya, Sierra Leone, Guinee da Najeriya, domin hana yaduwar cutar Ebola, haka kuma tafiye-tafiyen 'yan kasar Liberiya zuwa Ghana, musamman a sansanin Buduburam an gitta sharudan bincike.

Ta wani bangare, ofishin jakadancin Liberiya dake Accra ya bayyana cewa, gwamnatin Ghana ta aiwatar da wasu matakan bincike a cikin filayen jiragen sama, wadanda suka hada da yin rajista da yin bincike ga lafiyar dukkan fasinjojin da suka iso Accra daga kasashen da cutar Ebola ta fi shafa.

Ita ma gwamnatin Liberiya ta kafa irin wadannan matakan bincike a filin jirgin kasa da kasa na Monrovia-Roberts. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China