in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya ba da kusan dalar Amurka miliyan 200 domin yaki da cutar Ebola
2014-08-05 10:26:58 cri

Bankin duniya ya sanar a ranar Litinin cewa, zai ba da kusan dalar Amurka miliyan dari biyu bisa ga gidauniyar gaggawa domin taimakawa kasashen yammacin Afrika uku wato Guinee, Liberiya da Sierra Leone wajen yaki da cutar Ebola a wannan shiyya.

Shugaban bankin duniya, Jim Yong Kim ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa cewa, wannan sabon mataki na taimakon kudi an dauke shi ne domin amsa kiran wadannan kasashen Afrika uku da cutar Ebola ta fi shafa da kuma kiran Hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) wadda ta bukaci taimakon gaggawa domin shawo kan wannan annoba.

"Ina damuwa sosai kan sabbin mutanen dake cikin hadari, sai kuma idan za mu iyar dakatar da wannan cuta dake yaduwa cikin sauri." in ji mista Kim. Tare da yin kira ga gamayyar kasa da kasa wajen murkushe annobar Ebola da tuni ta kashe mutane 887 a wannan shekara.

Kim ya kara da cewa, "Na sani game yadda wannan annobar take yaduwa a ko wace rana, kuma na nuna bacin rai sosai kan labarin da na samu na cewa, cutar ta hallaka ma'aikatan kiwon lafiya, iyalai, da al'ummomi, haka kuma ta janyo rudani cikin zaman rayuwar jama'a da kawo rauni ga tsarin kiwon lafiya na wadannan kasashe uku."

Mista Kim ya yi wadannan kalamai a ranar farko ta dandalin Amurka da Afrika a birnin Washington. Tare da bayyana cewa, kudaden da aka alkawari za su taimakawa wajen sayan magunguna, biyan albashin ma'aikatan kiwon lafiya da sayen sauran kayayyaki masu amfani wajen ba da kulawa ga tsarin kiwon lafiya da kuma taimakawa al'ummomin da suka rasa kudin shiga dalilin wannan annoba. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China