Dangane da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Qin Gang ya bayyana a yau Laraba 30 ga wata cewa, gwamnatin kasar Sin na kiyaye 'yancin bin addini na jama'ar kasar bisa dokoki yadda ya kamata, kuma dukkanin jama'ar kasar suna da 'yancin addini bisa dokokin kasar. Kasar Sin ba za ta yarda da zargin da kasar Amurka ta yi mata ba game da wannan batu.
Sin ta kuma nuna bacin rai dangane da zargin da bai dace ba da Amurka ta yi kan manufofin addini na kasar Sin. Don haka ta yi kira ga kasar Amurka da ta kawar da bambancin ra'ayin siyasar da take nunawa kasar Sin, ta kuma daina tsoma baki cikin harkokin cikin gida na kasar Sin ta hanyar yin amfani da batun addini. (Maryam)