in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manyan limaman masallatan idi dake cikin birnin Kano a arewacin Najeriya sun bukaci samun Karin hadin kai tsakanin musulmi da kirista
2013-10-15 18:49:37 cri

Samada al`ummar musulmi miliyan bakwai ne suka gudanar da sallar idin layya yau 15 ga watan Okutoba a Jihar Kano dake arewacin Najeriya.

A hudubobin da suka gudanar daban daban, limaman sunce Najeriya zata cigaba da kasancewa kasa daya dunkulalliya idan har an samu Karin hadin kai tsakanin kabilu da mabiya addinai daban daban dake kasar.

Wakilin mu dake Kano ya halarci sallar idi a sabuwar jami`ar Bayero ga kuma rahoton daya aiko mana.

Auwal Abubakar shi ne ya jagoranci sallar idin a harabar sabuwar jami`ar Bayero inda masallata sama da dubu daya suka smau halarta.

An dai tayar da sallar ne da misalign karfe takwas da kwata, inda aka kammala da karfe tara saura kwata.

A hudubar daya gabatar, babban limamin ya bukaci al`ummar musulmi da su yi kokarin koyon darussan dake cikin wannan rana ta sallar layya, wadda take da mutukar mahimmanci a cikin addinin islama.

Ya bukaci musulmi dasu kasance masu kaunar zaman lafiya ako yaushe,inda yace zaman lafiya shine ginshikin cigaban kowacce kasa.

Rahotanni kuma daga babban masallacin cikin birnin Kano sun tabbatar dacewa Farfessa Sani Zaharaddeen shin e ya jagoranci sallar idin, inda shima hudubar tasa ta kunshi bukatar kyautata `yan uwantaka a tsakanin musulmi.

Mataimakin gwmanan Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje shine ya wakilci gwamna Rabi `u Musa Kwnakwaso wanda yake can kasar Saudiya domin aikin hajji.

Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero da dukkan yan majalissar sa sun halarci sallar idin nay au.

Idan dai za a iya tunawa a sallar bikin karamar sallah mai martaba sarkin Kano bai samu halarta ba sabo da rashin cikakken koshin lafiya.

Wani labari daya farantawa kanawa rai shine sanarwar da masarautar Kano ta yi nacewa a wannan karon mai martaba Sarkin Kano zai gudanar da hawan sallah kamar yadda aka saba.

A sallar data gabata dai mai martaban bai samu hawa ba sabo da rashin koshin lafiya wanda ya kais hi ga kwanciya a asibiti har na tsawon watanni uku a kasar dubai. (Garba bdullahi Bagwai)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China