in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Ghana na aiki tare don shawo kan hako ma'adinai ba bisa ka'ida ba
2013-06-19 10:22:35 cri

A ranar Talata ne wani babban jami'in kasar Sin ya bayyana cewa, kasashen Sin da Ghana na aiki tare kan batun Sinawa dake hakar gwal ba bisa ka'ida ba a kasar ta yammacin Afirka.

Jakadan Sin a kasar Ghana Gong Jianzhong ya bayyana wa taron manema labaru cewa, batun Sinawa dake hako ma'adinan gwal a kasar Ghana ba bisa ka'ida ba wata matsala ce a batun kara gina dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Jakada Gong ya ci gaba da bayyana cewa, Sin na dora muhimmanci kan wannan batu inda shi ne ma ya sa tana da tawagogi guda biyu a cikin watan Maris da Yuni zuwa kasar Ghana don tattaunawa da bangaren kasar Ghana da nufin samo yadda za'a warware wannan batu.

Ya ce, wannan mataki ya nuna kyakyawar aniya da kuma dagewar kasar Sin na ganin an warware wannan batu, ganin cewa, ta hanyar hadin gwiwa ne za'a cimma hakan.

A cikin watan da ya gabata ne shugaban kasar Ghana John Dramani Mahama ya kaddamar da wani kwamiti kan yaki da hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba da nufin cafkowa, gurfanarwa da kuma tisa keyar duk wani 'dan kasar waje da aka kama yana harkar hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba, kana a hukunta 'yan asalin kasar dake da hannu ciki.

Shugaban tawagar kasar Sin Qiu Xuejun ya ce, ko kadan kasar Sin ba ta yarda Sinawa su yi hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a kasar Ghana, kana ya yi kira ga gwamnatin kasar da ta mutunta, ta kuma kare hakkin 'yan asalin kasar Sin.

Ya kuma yi kira ga cibiyoyin tsaron kasar Ghana da su dakatar da hari da kuma fashi da akewa Sinawa masu hakar ma'adinai a kasar. (Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China