in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Musulmi a birnin Lanzhou na kasar Sin sun yi farin cikin sake zagayowar bikin karamar salla
2013-08-08 17:15:47 cri

Ranar 8 ga wata, rana ce da Musulmi a kasar Sin ke murnar zuwan babbar rana ta karamar sallah, wadda ke zuwa bayan kammala azumi har na tsawon wata guda, wannan lokaci ne da watan Ramadan ya zo karshe, kuma Musulmi ke farin cikin zuwan wannan rana. Domin karin bayani kan wannan batu, abokin aikinmu Bako ya hada mana wannan rahoto.

Bisa ga tsarin addinin Musulunci, watan Ramadan wata ne da Allah Ubangiji ya kebewa musulmi domin su azumce shi, bisa koyarwar Annabi Mohammed (SAW), kuma wannan wata ya zama wani wata mai tsarki da alheri. Ban da wannan kuma, azumi ya kasance daya daga cikin muhimman rukunai 5 da suka wajaba a kan ko wane Musulmi, wato Tauhidi, da Zakka, Salla, Azumi, da Hajji. Mataimakin shugaban kwamitin addinin Musulunci na birnin Lanzhou, kuma limamin masallacin Xin Guan da ke birnin Lanzhou Ma Jun ya bayyana cewa, bisa ga tsarin addinin Musulunci, azumi ya kan kawo tsarki da daukaka ga jama'a. Ma'anar watan Ramadan ba wai kawai yana nufin kammala wani aikin ibada ba ne kadai, domin kuma azumin yana kawo tsarki ga halayyar jama'a, da hana kwadayi, da jin radadin talauci, da kara nuna tausayi ga mabukata, da taimakawa matalauta, da yin zakka ga sauran mutane. Sabo da haka, ya ce ya kamata ko wane Musulmi ya san ma'anar watan Ramadan, ya ce, "Ya kamata mu fahimci addinin Musulunci sosai, sannan, mu san matakan da za mu dauka, yanzu, wasu Musulmi a duniya sun mayar da azumi tamkar wani aiki ne kawai da za su kammala shi, lallai, ba su fahimci abin da ya dace mu koya daga azumi ba, ba su san maslaha da yake kawowa ba. Ina zato ya kamata mu kara fahimtar wannan. Alal misali, salla da azumi, me ya sa muke yin su? Wato azumi shi yana kawo mana radadi na yunwa, kuma ya sa mu kara jin dadin abinci, sannan mu san irin bukatun abinci ga matalauta ke da ita, ba wai a kammala shi kawai ba."

Bayan da aka kammala azumin watan Ramadan na tsahon wata guda, duk masallatai, manya da kanana, suka shirya kasaitaccen biki domin murnar wannan rana, da taya Musulmi na duniya murnar kammala ibada cikin nasara. Musulmi su kan sa tufafi na gargajiya, don nuna farin cikinsu, da nuna godiya, da yabo ga Allah Madaukakin Sarki. A masallacin Xin Guan, da ke birnin Lanzhou, Musulmi da suka halarci Sallar idi, sun nuna farin ciki sosai, inda Liman Ma Jun ya bayyana cewa, "Yau, a ciki da wajen masallaci, har zuwa titin da ke kusa da wannan masallacin, ya cika da mutane sosai, inda wasu ma suka yi salla a kan titi."

Musulmi a duk fadin duniya na farin ciki da murna game da wannan rana. A wannan rana, Musulmi kan taru, don yi wa juna murnar sake kewayowar wannan muhimmiyar rana. Wasu mabiya addinin na Musulunci da ba su gida, kan yin kokarin gaggauta komawa gida, domin yin wannan biki tare da iyalinsa. Wani Musulmi mai suna Zhou Wenqing, da yake zaune a birnin Lanzhou, wanda kuma ke da jika da ke karatu a birnin Boston na kasar Amurka, da kuma babban jikansa dake karatu a kasar Turkiyya, dukkansu sun koma gida, domin halartar bikin Sallah na bana. Babban jikansa Zhou Bolin dan shekaru 20 da ke karatu a birnin Istambul na kasar Turkiyya, ya fada wa wakilinmu cewa, karamar salla na da ma'anar musamman ga ko wane musulmi, ya ce,"Ga ko wane Musulmi, lokacin karamar Sallah, lokaci ne na wani babban biki, bayan kammala azumi har na tsawon wata guda, a bikin karamar salla, musulmi kan taru, domin gudanar da bikin wannan babbar rana, bikin yana da ma'ana ta musamman gare su. A sa'i daya kuma, ba ya ga haduwar da ake yi, don taya juna murna, ana kuma amfani da wannan lokaci wajen nuna yabo da godiya ga Allah Ubangiji bisa ni'imominsa ga al'ummar ta Musulmi."(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China