An yi bikin murnar cika shekaru 60 da kafa hukumar kula da harkokin addinin Musulunci na Sin
A ranar Jumma'a 30 ga wata ne, aka yi bikin murnar cika shekaru 60 da kafa hukumar kula da harkokin addinin Musulunci na Sin a babban dakin taron jama'a, inda zaunannen memban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na JKS, kana shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta Sin, Yu Zhengsheng ya gana da shugabannin hukumar, tare da daukar hotuna da duk wakilan hukumar. Yu ya taya murnar cika shekaru 60 da kafa wannan hukuma, tare da jinjinawa dukkan wakilai da musulman da ke nan Sin. Da fatan za su kara kokarin yin nazari kan addinin, da ba da gudummawa wajen bunkasa kasar Sin a fannoni daban daban.(Fatima)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku