Dangane da rahoton da ke bayyana rashin 'yancin aiwatar da addini yadda ya kamata ga mabiya a kasar Sin da Amurka ta fitar, Madam Hua ta ce, ya kamata kasar Amurka ta dubi nata matsalolin ta daina tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan wassu kasashe tana fadin kalaman da ba su dace ba.
Hukumar kula da tafiyar da addini cikin 'yanci ta kasar Amurka a cikin rahotonta na shekara shekara da ta fitar ranar Talatar nan, ta ce 'yancin gudanar da addini a kasar Sin ya kara munana a shekarar da ta gabata. Tana mai bada shawara ga kasar Amurka da ta rubuta kasar Sin a cikin jerin kasashen da suke da damuwa game da 'yancin addini matuka.
Madam Hua ta ce, Gwamnatin kasar Sin tana kare al'ummarta tare da ba su damar gudanar da addininsu kamar yadda dokar kasa ta tanada, don haka in ji ta, Sin na bada shawara ga wannan hukumar ta Amurka da ta mutunta gaskiya ta kuma watsar da daukar aikin da ba na ta ba tare da daina fakewa da addini domin tsoma baki a cikin harkokin cikin gidan Sin.
Haka kuma Kakakin harkokin wajen na Sin ta shawarci Amurka da ta karanta bayanin 'yancin dan adam na Amurka na shekara ta 2012, wanda cibiyar yada labarai ta kasar Sin ta fitar.(Fatimah Jibril)