Musulman Sin za su tsaya tsayin daka wajen yaki da masu tsattsauran ra'ayin addini
Kungiyar addinin Musulunci ta kasar Sin ta kira taron kara wa juna sani game da koyarwar addinin Musulunci a birnin Urumqi dake jihar Xinjiang daga ranar 14 zuwa 15 ga wata, wanda aka mai da "tsayawa tsayin daka kan sassaucin ra'ayi da kawar da tsattsauran ra'ayi" a matsayin babban takensa. Shugabannin kungiyar addinin Musulunci da limamai da kuma wasu masanan da abin ya shafa kimanin dari daya ne suka halarci taron, inda suka yi bayani kan koyarwar addinin Musulunci da suka hada da kishin kasa, zaman daidaituwa, hadin kai da dai sauransu, kuma sun yi Allah wadai da ra'ayoyin masu tsattsauran ra'ayi da kuma hare-haren da 'yan ta'adda suka kai.
Bugu da kari, an zartas da wata takarda kan tsayawa tsayin daka kan sassaucin ra'ayi da kawar da tsattsauran ra'ayi a yayin taron, don yin kira ga musulmai da su tsaya tsayin daka kan bin koyarwar addinin Islam, da kula da abubuwan da suke yi da maganganun da suke fada, kana da yaki masu tsattauran ra'yi, a kokarin ba da gudumawarsu ga kiyaye hadin gwiwar kabilu daban daban, sa kaimi ga sulhuntar addinai daban daban, da kuma bunkasuwar kasar Sin. (Maryam)