Jiya ranar Lahadi 3 ga wata, kamfanin kasar Sin ya cimma nasarar kammala tushen wani aikin mafi girma da kamfanin kasar Sin ya ba da taimako wajen gina shi a Afrika, wato hasumiyar Mi'dhanah ta masallacin Alger na kasar Aljeria.
Kamfanin gine-gine na kasar Sin shi ya kula da wannan aiki da ya shafi kudi dala biliyan 1.5, wanda ya kasance aiki mafi girma da masana'antun kasar Sin ke yin kwangilar gina shi a Afrika. Kuma yana kunshe da gine-gine 12, daga cikinsu hasumiyar Mi'dhanah mai tsayin mita 264 za ta zama gini mafi tsayi a Afrika, kuma ta kasance irinta mafi tsayi na masallaci a duk duniya.
Wannan aiki kuma ya kasance aikin da ya shafi kudi mafi yawa a cikin wata kwangilar da aka kulla a shekarar 2011 a duniya, bayan kammalarsa a shekarar 2015, ba shakka zai jawo hankalin kasashen da dama sabo da ba ma kawai ya kasance wurin ibada ba, har ma zai jawo hankali masana, masu fasaha da masu yawon shakatawa. (Amina)